Kasar China ta gargadi ‘yan kasarta da zuwa nahiyar Nageriya mai hadarin garkuwa da Mutane.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta gargadi ‘yan kasar Sin da kamfanonin da ke aiki a Afirka kan yin balaguro zuwa wasu yankuna masu hadari sakamakon sace ‘yan kasar Sin da ake yi a nahiyar.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, a yau ranar Litinin din nan, ya tabbatar da sace wasu ‘yan kasar Sin biyar a jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, inda ma’aikatar ta bukaci wadanda ke wurare masu hadari da su gaggauta ficewa.

Mista Zhao ya ce an yi garkuwa da mutanen ne a yayin wani hari da aka kai kan wata ma’adanin zinari a kauyen Mukera da ke gabashin Kongo, ya kara da cewa a wani lamari na baya-bayan nan da ya faru a Najeriya, an kuma yi garkuwa da ma’aikatan kasar China uku.

Mai

magana da yawun ya jaddada cewa akwai “gagarumar hadarin tsaro” a Najeriya da Kongo, kuma wadannan al’amura ba su kasance na farko ba.

Kakakin ma’aikatar ya ce “A baya ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, da ofisoshin jakadancin sun shawarci ‘yan kasar da kada su je wuraren da ke da hadari.”

Kasar Sin ta kara yawan jarin da take zubawa a masana’antar hakar ma’adinai a Afirka a cikin ‘yan shekarun nan.

Hakan ya haifar da karuwar kyama ga ma’aikatan kasar Sin masu hannu da shuni da ke aiki a kasashe irin su Kongo mai arzikin albarkatun kasa, inda yanayin rayuwa ya yi kadan.

A shekara ta 2008, tsohon shugaban kasar Congo Joseph Kabila, ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya mai cike da cece-kuce ta dala biliyan 9, wadda ta baiwa kasar Sin hakkin hako ma’adinai a kasar, domin samun kudaden gudanar da ayyukan more rayuwa da ake bukata a kasar

NAN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *