Kasar Ingila ta Hana turawanta zuwa jihar Kano da katsina idan sunzo Nageriya.

Mahukunta a kasar tarayyar Burtaniya sun fitar da sanarwar gargadin yan kasar da ke duka fadin duniya kuma musamman ma wadanda ke Najeriya kan zuwa jihohi 12

Kamar yadda muka samu, kasar ta Birtaniya ta bayyana dalilai na rashin tsaro da kuma yiwuwar tayar da hatsaniya a yan lokutan nan a matsayin dalilan ta na fitar da wannan sanarwa.

Majiyarmu ta katsina Post ta samu cewa sauran jihohin da kasar ta Birtaniya ta gargadi ya’yan ta akan zuwa sun ha’da da jihar Katsina da Borno, Yobe, Adamawa, Gombe, Kaduna, da kuma Zamfara.

Sauran

kuma sune Delta, Bayelsa, Rivers, Akwa Ibom da kuma jihar Cross River.

Haka zalika kasar ta yi gargadi ga ya’yan kasar kan zuwa jihohin Bauchi, Kano, Jigawa, Niger, Sokoto, Kebbi, Abia da Kogi idan ba ya zama dole ba.

Yayin da rashin tsaron da ya shafi yan bindiga ke da nasaba da hana zuwa jihohin Arewa, yayinda a kudancin Nageriya matsalar yan aware na yan Biafra ta Hana Zuwa Kamar yadda sanarwa ta nuna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *