Kawo yanzu a wannan shekara ta 2021 mun kashe bilyan sha biyar 15.7bn domin samar da ruwan Sha ~cewar Gwamnatin katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta ce ta kashe Naira biliyan 15.7 a wannan shekara ta 2021 domin daidaitawa da gyarawa da kuma shigar da magudanar ruwa zuwa garuruwan Katsina, Funtua, Malumfashi da Jibia.

Wannan yana kunshe ne a cikin takardar kudirin kasafin kudin gwamnatin Katsina na 2022 da aka mika wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Litinin.

Takardar ta nuna cewa ana gudanar da aikin ne a karkashin Hukumar Kula da Yasawar Ruwa ta Najeriya, Nigeria Erosion and Watershed Management Project (NEWMAP).

samar

da wannan magudanun ruwa na iya kawo karshen Matsalar ruwan Sha a yankunan dake fama da Matsalar ta ruwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *