Kawo Yanzu mun bawa talakawan Nageriya Tallafin Bilyan dari 100bn ~Cewar Gwamnatin Buhari.

Gwamnatin Tarayya ta bakin Karamin ministan kwadago da samar da aikin yi Festus Keyamo, ta ce gwamnatin tarayya ta kashe Naira biliyan 100 ga matasa marasa aikin yi a kasar nan.

Mista Keyamo ya yi wannan ikirarin ne a wata sanarwa da ofishin yada labaran sa ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

Ministan wanda ya samu wakilcin Darakta Janar na Hukumar Samar da Ayyukan yi ta kasa (NDE), Abubakar-Nuhu Fikpo, ya bayyana haka ne a lokacin kaddamar da rabon kayayyakin tallafi ga mata a garin Jos na jihar Filato.

A

cewar Minisatan Naira biliyan 100 an bayar da su ne ta bankin raya kasa na Najeriya daga shekarar 2017 domin saukakawa masu kanana da matsakaitan masana’antu (MSMEs) da nufin samar da ayyukan yi ga marasa aikin yi a kasar.

“Tun a shekarar 2017, Bankin Raya Kasa na Najeriya ya fitar da jimillar Naira biliyan 100 ta hannun cibiyoyin hada-hadar kudi na bankin (PFIs) guda 27, wanda hakan ya yi tasiri ga ma’aikata sama da 100,000.

“Abin farin ciki ne a lura cewa kashi 52 cikin 100 na rancen da aka bayar a shekarar 2019 da 2020 sun kasance ga matasa da kasuwancin mata,” in ji shi.

Mista Keyamo, a lokacin da yake jawabi ga wadanda suka ci gajiyar shirin, ya bayyana cewa an tsara shirin karfafawa mata NDE ne don tabbatar da cewa wadanda suka ci gajiyar shirin da wadanda aka koyawa sun samu sana’o’in da suka dace da kasuwa da za su zaburar da su wajen fara sana’o’insu.

“Manufarmu ita ce mu samar musu da hanyoyin samar da kudaden shiga cikin gaggawa saboda rawar da suke takawa wajen bayar da tallafin iyali da zaman lafiyar al’umma da tushen al’umma,” in ji shi.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *