KISHIN AL’UMMA: Bamanga Ya mallaka dukiyarsa ga taimakon Al’ummar domin koyi da Ayyukan Gwamna zullum a jihar Boron.

Biyo bayan Kudirori goma Sha biyu 12 na Gwamnan Jihar Borno: Farfesa Engr. Babagana Umara Zulum mni FNSE: a yunkurin sa na dawo da zaman lafiya da tsaro da ayyukan zamantakewar Al’umma tare da tattalin arziƙi da sake gina Jihar borno harma da gyara tare da maido da al’ummomi daban-daban waɗanda ka iya ganin su a kowane yanki na jihar Borno,

Sanatan dake da kudrin shigowa amatsayin Mai wakiltar Borno ta Kudu bisa yardar Alh: Aliyu Muhammad Lawan Buba (Bamanga) shi ma ya shiga layin wannan na kyakkyawan aiki mai girma, a kokarin sa na koyi da abin yabonsa da ƙwazon Farfesa Engr Babagana Umara Zulum ta Hanyar bayarda gudummawarsa Wacce babu adadin musamman a bangaren samar da kayan aikin asibiti kamar katifu da zannuwan gado matashin Kai da Sauran kayan bukatun Yau da kullum, Zuwa ga Yankin Hawul, Askira Uba, Damboa da Chibok.

Bayan

Haka Kuma Alh Aliyu Bamanga ya ba da gudummawa sosai wajen samar da kayan abinci da sauran abubuwan da bsu shafi abinci ba ga al’ummar Limankara da ke ƙaramar hukumar Gwoza, ya ba da magunguna domin agajin gaggawa ga al’ummar Garin Pulka yayin barkewar cutar kwalara, Har’ila Yau kuma a kwanan nan ya fara aikin gyaran babbar hanyar da ta haɗa Damboa, Chibok, Askira Uba da Hawul Duk domin taimakon Al’ummarsa dake fama da Matsalolin rayuwa na yau da kullum

A daidai Lokacin da Gwamnan Jihar borno ke kokarin dawo da Zaman lafiyar Jama’a da Cigaba ta Hanyar Samar da Ayyukan yi ga matasa ana bukatar matasa masu kishin Al’ummar jihar kamar yadda Gwamna ke kokari Hakan yasa Alh Aliyu Muhammad Lawan Buba Bamanga Mai neman ‘dan majalisar dattijan Mai wakiltar Borno ta Kudu ke Shan yabo daga bakin Al’ummar Jihar borno musamman yadda yake koyi da Gwamna zullum a fannin Ayyukan sa na alkhari ga Jama’a da basu karewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *