Kotu ta amince a bayyana ‘yan Bindiga amatsayin ‘yan ta’adda ~Cewar Minisatan shari’a Abubaka malami.

Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya ce kudirin Gwamnatin Tarayya na murkushe ‘yan fashin ya kare a yanzu da kotu ta amince da bukatar da ofishinsa ya shigar na bayyana kungiyoyin ‘yan bindiga a matsayin kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Kakakin Ministan Umar Gwandu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Yau ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce, sanarwar na nuni ne da yadda ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya da ma gwamnatin tarayya ke bin ka’ida kamar yadda doka ta tanada.

“Ci

gaban yana nuni ne ga kudurin Gwamnatin Tarayya na bin ka’idojin kasa da kasa wajen mutunta ka’idojin shiga yaki da ta’addanci, kungiyoyin ‘yan aware, ‘yan tada kayar baya da kuma ‘yan bindiga a kasar nan,” in ji shi.

Ya ce ta wannan sanarwar ne gwamnatin tarayyar Najeriya ta dauki kwarin gwiwar daukar matakai na musgunawa duk kungiyoyin ‘yan ta’adda da masu daukar nauyinsu a kokarin da ake na ganin an magance dimbin kalubalen rashin tsaro a kasar nan.

Ofishin Babban Lauyan Tarayya da Ministan Shari’a tare da hadin gwiwar hukumomin gwamnati da suka hada da jami’an tsaro suna aiki tukuru don yin abin da ya dace domin kawo karshen ta’addanci a Nageriya.

Gwamnatin Tarayya za sanarwa Jaridu Kan kudrin odar haramta wannan hanyar ta ‘yan Bindiga inji Sanarwar

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *