Kotu Ta Tsare Mutane Biyu a Gidan Yari Saboda Sun Zargi Tsohon Shugaban Kasa Abdulsalamu Da Samarwa ‘Yan Ta’adda Makamai.

Jude Akaeze, dan sanda mai gabatar da kara, ya gabatar da tuhume-tuhume hudu a kan wadanda ake tuhumar, Abdulkareem Ajibola da Anas Umar.

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Minna, Jihar Neja ta tasa keyar wasu mutane biyu zuwa gidan yari saboda buga wata mummunar sanarwa a kan kafofin yada labarai kan tsohon Shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar.

Jude Akaeze, dan sanda mai gabatar da kara, ya gabatar da tuhume-tuhume hudu a kan wadanda ake tuhumar, Abdulkareem Ajibola da Anas Umar, in ji Barista NG.
Abdulsalami

Abubakar
Akaeze ya ce wadanda ake tuhumar sun sabawa sashe na 24 (1b) na dokar aikata laifuka na cafe.

Dan sanda mai gabatar kara ya roki a dage sauraron karar don ba shi damar gabatar da shaidu, don tabbatar da zargin da yake yi wa wadanda ake tuhumar.

Amma, lauyan da ke kare, Abdulkareem Abubakar ya nemi a ba da belin, yana mai cewa wadanda suke karewa sun riga sun zauna na wata daya a cibiyar gyara kuma sun musanta aikata laifuka hudu.

Sai dai, Alkalin da ke jagorantar shari’ar, Mai Shari’a Emeka Nwite ya bukaci lauyan da ke kare shi da ya nemi belin.

Daga nan ya dage sauraron karar zuwa 26 ga Yuli, 2021, don fara shari’a yayin da za a ci gaba da tsare wadanda ake zargin a cibiyar gyara.

Ana tuhumar wadanda ake tuhumar ne da bugawa da yadawa a kafafen sada zumunta cewa Abdulsalami ya mallaki wani jirgi mai saukar ungulu da ake zargin an kame a kusa da Erena a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja da ke samar da makamai da sauran kayan aiki ga ‘yan fashi da ke addabar jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *