kotun abuja ta saka ranar alhamis domin yanke hukunci Kan shari’ar sarki Sanusi da Ganduje.

Babbar kotun tarayya dake Abuja ta sanya ranar Alhamis Talatin ga watan Nuwamba domin yanke hukunci kan karar da Sarkin Kano na 14 Khalifa Muhammad Sunusi II ya shigar gabanta yana mai kalubanatar tsare shi da aka yi bayan da aka tube shi daga kujerar Sarautar Kano.

A ranar 12 ga watan Maris na shekarar 2020 ne Mai Martaba Sarkin Kano na 14 Khalifa Muhammad Sunusi II ya shigar gaban babbar kotun tarayya dake Abuja yana mai karar Sifeton ‘yan sanda na kasa da babban daraktan hukumar tsaro ta farin kaya SSS da kuma Gwamnatin Kano, kan tsare shi da aka yi inda ya nemi a biya masa hakkinsa.

Tun

a lokacin kotun tayi hukunci kan cewar tsare Sarkin da kuma tura shi garin Loko a jihar Nasarawa, kotun ta bada umarnin a saki Sarki Muhammadu Sunusi daga tsarewar da akai masa a jihar Nasarawa, ta kuma bayyana cewar ba daidai bane abinda akai masa.

Tun a lokacin dai ake cigaba da Shariah har kawo wannan lokacin da kotun ta sanya ranar da zata yi hukunci na karshe. Daga daily Nigeria Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *