Ku bayyana ‘yan Bindiga amatsayin ma’aikatan Gwamnatinku tunda ba zaku iya bayyana su amatsayin ‘yan ta’adda ba ~Shehu sani ga Gwamnatin Buhari.

Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bukaci gwamnati ta ayyana ‘yan bindiga a matsayin ma’aikatan gwamnatin tarayya tunda ta kasa kallon su a matsayin ‘yan ta’adda.

Sani ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter yayin da yake kokawa kan yadda ‘yan bindiga ke kashe mabiya addinin Kirista da Musulmi a gidajensu.

Ya wallafa a shafinsa na twitter cewa, “Sun kashe musulmi masu ibada a masallatan su a jihar Neja da Katsina; sun kashe kiristoci a Cocin su dake jihar Kaduna; idan Gwamnati ba ta son bayyana su a matsayin ‘yan ta’adda, to ta ayyana su a matsayin ma’aikatan gwamnatin tarayya.”

class="sharedaddy sd-sharing-enabled">

Share this:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *