Ku cire tallafin man fetir sarki Muhammadu Sanusi Lamido ya shawarci Gwamnatin Tarayya.

Tsohon Sarkin Kano muhammad Sanusi II, ya ce gwamnatin tarayya na tafka laifuka ta hanyar biyan kudaden tallafin man fetur daga asusun Gwamnatin tarayya.

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi wannan magana ne a matsayinsa na mai ba da shawara kan manufofin ci gaba mai dorewa ga (SDGs) a taron tattalin arzikin Najeriya da aka kammala a Abuja.

Ya kuma ce hanyoyin da ake amfani da man fetur a Najeriya a kullum yasa ake samun cin hanci da rashawa a cikin kudaden tallafin man fetur.

Lamido

yace “Wannan kudin da ke fitowa daga man fetur na asusun tarayya ne, kuma gwamnatin tarayya ba ta da ‘yancin biyan tallafi a madadin tarayyar Nageriya.

“Don haka al’amari ne da ya shafi tsarin mulki domin wannan kudi ne da ya kamata a kai ga matakin tarayya, jihohi da kananan hukumomi domin magance Matsalar Al’umma Muna bukatar dakatar da wadannan batutuwan,” inji shi.

Ya kuma bayar da shawarar kawo karshen tallafin man fetur din da kuma tallafin wutar lantarki, inda ya ce kamata ya yi a saka kudaden da aka tara a wasu sassa masu muhimmanci kamar ilimi da kiwon lafiya ya kara da cewa ribar da aka samu na dogon lokaci ya zarce radadin da za aji na gajeren lokaci yayin janye tallafin

Sarkin Yace “Na taba fadin haka tun a matsayina na Gwamnan CBN a gwamnatin da ta shude. Abin da na ce ba nauyin wata gwamnati ba ne ace ta dauki nauyin tallafin man fetur.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *