Labarai

Ku Fara Duban Jinjirin Watan Shawwal Ranar Juma’a-Sarkin Musulmi

Spread the love

Sarkin Musulmi Ya Bukaci Al’ummar Musulmin Najeriya Dasu Fara Duban Jaririn Watan Shawwal Daga Ranar Juma’a

Majalisar Koli kan Harkokin Addinin Musulinci Ta Kasa NSCIA, Karkashin Jagorancin Maigirma Sarkin Musulmin Najeriya, Alhaji Sultan Sa’ad Abubakar Na Uku, Ta Bukaci Daukacin Al’ummar Musulmin Najeriya Dasu Fara Duban Jaririn Watan Karamar Sallah Na Shawwal Daga Ranar Juma’a 22 Ga Wannan Watan Na Mayu Da muke Ciki,

Mataimakin Secretary General Din Majalisar Koli kan Harkokin Addinin Musulinci Ta Kasa, Salisu Shehu ne yabayyana Hakan a Ranar Litinin a  Birnin Tarayya Abuja,


Sannan Malam Salisun ya taya Jama'ar Musulmi Murnar Ganin Wannan Azumi Na Ramadan Din Shekara Ta 1441 Bayan Hijira, Tareda Fatan Allah yanuna Mana Azumin Badi Da Rai Da Lafiya,

A jawabin nasa Malam Salisu ya Bayyana Cewar “Biyo Bayan Tattaunawar Da Mukayi Da Kwamitin Masu Ganin Wata Na Kasa NMSC, Sun Bayyana Ranar Juma’a 22 Ga Watan Mayun Wannan Shekara Ta 2020 Wanda Yayi Dai – Dai Da 29 Ga Watan Ramadan 1441 a Matsayin Ranar Da Za’a Fara Duban Jaririn Watan Shawwal, Biyo Bayan Kammala Azumin Watan Ramadan kwanaki 29”.

To Addu’ar Mu Dai Anan itace Allah ya Azurtamu Da Ganin Wannan Wata Mai Albarka Lafiya,

Sannan Allah ya Fitar Damu Daga Cikin Kuncin Da Muka Shiga a Sanadiyyar Wannan Annoba Ta Covid - 19, Albarkacin Wannan Wata Mai Albarka Na Ramadan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button