KU KARANTA DA ZAFI-ZAFI: Jam’iyyun Adawar Najeriya sun yi kira da’a tsige Buhari, Lawan da Gbajabiamila.

Hadaddiyar Gamayyar Jam’iyyun Siyasa (CUPP) ta bukaci Majalisar Dokoki ta kasa da ta farashirin tsige Shugaba Muhammadu Buhari.

Mai magana da yawun, Ikenga Imo Ugochinyere ne ya yi wannan kiran a ranar Laraba a wani taron manema labarai da suka gudanar.

Ya yi zargin cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ci zarafin ofishinsa, sannan ya aikata ba daidai ba kuma ya kasa kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.

Ugochinyere

ya ce yanzu rayuwa ta yi tsada a Najeriya wanda har yanzu shugabanni “ba sa nuna tausayawa”.

CUPP ta ce mutane ba su da tausayi tunda kisan gilla ya zama ruwan dare kuma ana daukar kowanne sakon sabon mutuwa da wasa.

Jam’iyyun sun yi kira ga ‘yan majalisar adawa da su yi aiki “cikin kawance da mambobin kishin kasa da ke a cikin APC dan neman ‘yanci gamida fara aiwatar da tsige Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan da Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila nan take”.

CUPP ta yi zargin cewa dukkanin shuwagabannin majalisun dokokin kasa sun gaza jagorantar abokan aikin su don yin aiki a matsayin kishin kasa.

“Ba su da sauran girmamawa saboda membobin zartarwa da yawa sun yi watsi da su ko da an gayyace su a hukumance.

Ba a mutunta ‘yan majalisa yanzu kuma ana watsi da su koda lokacin da suke kiran jami’an zartarwa a hukumance saboda sun zama yan amshin shata inda zaka gansu suna yawo daga wannan ofis yau da kullun zuwa ofis wani ofis din suna bara, cin zarafi, kwace komai da duk abin da za su iya kamawa.”

Ugochinyere ya sanar da cewa, CUPP ta shigar da kara a babbar kotun tarayya don neman umurnin mandamus don tursasa Majalisar Dokoki ta kasa ta gudanar da aikin ta na kundin tsarin mulki ta hanyar bincikar zarge -zarge da dama na rashin da’a da aka yi wa Buhari.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *