Kungiyar ta’addancin Boko Haram sun kashe Sojojin Nageriya talatin 30 a Borno.

Sojoji da dama da ke kan hanyarsu ta zuwa Maiduguri a ranar Juma’a wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne da ke da alaka da kungiyar ISWAP sun yi musu kwanton bauna, kamar yadda majiya mai tushe ta shaida wa Vanguard.
Lamarin ya faru ne a tsakanin karamar hukumar Marte- da Dikwa, a lokacin da maharan suka harba roket Launchers a kan manyan motocin soji wanda ya kai ga harbe-harbe, inda suka kashe sojojin da ake turawa daga karamar hukumar Marte zuwa Maiduguri.
Marte

mai nisan kilomita 180 daga arewa da Maiduguri ta kasance daya daga cikin yankunan karamar hukumar Borno da babu mazauna farar hula sakamakon galibin mutanenta sun yi hijira kuma sun samu mafaka a Monguno, da wasu sassan Maiduguri.

Wata majiya mai tushe da farko ta shaida wa Wakilinmu cewa sojoji 16 ne suka rasa rayukansu a cikin kwanton baunar, amma daga baya an samu labarin a yammacin ranar Asabar daga wata majiya cewa “kimanin sojoji 30 aka kashe tare da jikkata wasu da harbin bindiga”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *