Kungiyar ‘yan ta’adda ta IPOB ta mai da martani game da zargin da ake mata na kashe Ahmad Gulak, wani Jigo a Jam’iyar APC.

Kungiyar mutanen Biafra ta IPOB tace batasan komai ba game da mutuwar Ahmad Gulak wani jigo a jam’iyar APC Wanda aka kashe a Jihar IMO.

Kungiyar tace zargin ta da kashe Ahmad Gulak daidai yake da aibanta lokacin da ‘yan ta’adda sanye da kayan jami’an tsaro ke aikata muna nan abubuwa a kudu maso gabas.

An rawaito yadda aka kashe tsohon Hadimin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan a ranar Lahadi a Owrrri Babban birnin Jihar IMO yayin daya dawo Abuja.

Ahmad

Gulak yabar dakin sa a Otel a protea batare daya sanar da ‘yan sanda ko hukumomin tsaro ba saboda lamuran tsaro Na kudu maso gabas.

Majiyar mu ta hango wani jigo daga kungiyar ta IPOB mai suna Emma powerful Wanda shine kakakin kungiyar ta IPOB yana watsi da zargin da zargin da ake alankata kungiyar da mutuwar Ahmad Gulak, kuma ya nemi hukumomim tsaro da su binciki lamarin da wuri.

Emma powerful yace kafin Alakanta kungiyar IPOB kamata yayi hukumomin tsaro sufara bincikar mai masaukin Gulak, hope Ozodima da kuma abokan hamayyar sa Na siyasa don tabbatar da yiwuwar sa a hannun su. Inji kakakin kungiyar ta IPOB mai suna Emma powerful.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *