Kwankwaso a shekaru 65: Ganduje ya taya Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso murnar ranar haihuwa. (Na kasance mai ɗorawa daga inda ka tsaya, ina da tabbacin cewa gudunmawarka da tawa ta zama ummul-aba’isin ingiza cigaban jihar mu).

Kwankwaso da Ganduje

A yayin da tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jagoran darikar Kwankwasiyya ta duniya wato Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso ke bikin cika 65 a duniya, mutane da yawa sun ɗauki lokaci da biro wajen rera begen yabo ga Kwankwaso tare da masu fatan Alkairi.

CiKi kuwa harda gwamnan Kano mai ci a yanzu, wato Dr. Abdullahi Umar Ganduje. Inda ya sayi shafi guda sukutum a jaridar Daily Trust, domin taya shi murnar.

class="has-text-align-justify">A cikin sakon taya murnar, wanda shi yafi ɗaukan hankali, an jiyo gwamnan yana faɗin cewa:

“Tabbas, gagarumin abin da ka cimma a lokacin da kana gwamna nake mataimakin ka, na kasance mai ɗorawa daga inda ka tsaya, ina da tabbacin cewa gudunmawarka da tawa ta zama ummul-aba’isin ingiza cigaban jihar mu, da ɗaga darajar jin daɗin zamantakewa na ƴan jihar Kano”.

Abinda yake bawa mutane mamaki bai wuce yadda Ganduje yake ɗaukar lokaci wajen yiwa Kwankwaso fatan alkairi a duk lokacin da yake bikin ranar haihuwar sa, duk da sabanin siyasa da yake tsakanin su.Dr. Rabiu Musa Kwankwaso a shekaru 65.

Bugu da ƙari, wasu na ganin cewa tsakanin jagororin biyu, da wuya idan akwai gabar da ake tunanin da akwai.

Siyasa ce kawai tsagoranta.

Wasu kuma na mamakin yadda Ganduje yake ikirarin cewa ya daura akan inda Kwankwaso ya bari, inda wasu ke bada misali da barin tituna da Kwankwaso yakeyi a karamar hukumomi guda arba’in da hudu, da kuma barin makarantar kangararru da yayi a Kiru.

Koma dai menene, fatan alkairi zamuyi ga waɗannan jagorori. Shekaru masu albarka garesu.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *