LABARI DA ƊUMI-ƊUMI: Hakikanin Rashin lafiyar da ke damun Maryam Yahya

Jaridar Dokin Ƙarfe TV ita ce ta fara kawo wa labarin rashin lafiyar fitacciyar jaruma a masana’antar Kannywood, Maryam Yahya wanda a sanadiyyar ɓullar labarin daga gare mu, wasu sun fara yaɗa jita-jita da labarai marasa tushe akan asalin rashin lafiyar jarumar.

A binciken da mu ka gudanar, mun samu tabbacin cewa Maryam Yahya ta gamu da rashin lafiya wanda ake zargin asiri aka yi mata. Wannan shi ne haƙiƙanin abin da ya haifar mata da rashin lafiyar da ta ke ciki.

Duk wani labari da wasu za su faɗa akan rashin lafiyar jarumar ba wannan ba, to ba gaskiya ba ne, saboda haka jama’a su guji yaɗa jita-jita da labarai masa tushe da makama. Kamar yadda majiya mai tushe ta tabbatar mana rashin lafiyar jaruma Maryam Yahya ya na da alaƙa ne asiri ko jifanta da ake tunanin magauta sun yi.

Daga, Ahmad Aminu Kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *