Lasisin direbobi: Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa zata fara yiwa masu neman izinin tuƙi jarrabawa irin ta Jamb.

Yadda jarabawar zata dinga kasancewa kenan

Hukumar Kiyaye Haddura ta ƙasa (FRSC) ta ba da umarnin fara yiwa masu neman izinin tuki amfani da na’ura mai ƙwaƙwalwa (CBT) a matsayin wani mataki da hukumar tace zai kasance a kafatanin ofisoshin ta rassa rassa dake ƙasar.

Corps Marshal, FRSC, , Dr Boboye Oyeyemi ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da jami’in kula da ilimin jama’a na hukumar (CPEO), Mista Bisi Kazeem, ya fitar a ranar Juma’a a Abuja.

class="wp-block-image size-large">
Dr Boboye Oyeyemi

Oyeyemi ya ce wannan wani babban yunƙuri ne na bunƙasa mutuncin lasisin direbobin ƙasar nan.

Kamar yadda ya sanar, in ji shi, tsarin za a yi shi ne ta hanyar Inganta Makarantar Motsa Jiki (DSSP) don kawar da duk wani haɗari na haɗarurrukan hanya da ke faruwa sakamakon mummunar al’adar amfani da hanya.

Ya ƙara da cewa an fara gwajin na’ura mai ƙwaƙwalwa ga masu neman lasisin tuki a duk faɗin ƙasar daga 1 ga Yuni, 2021, saboda haka, ana buƙatar jama’a su sani.

A cewarsa, ana sa ran mai neman lasisin ya yi amfani da lambar da za’a bashi bayan ya kammala karatun kwas ɗin da zai ɗauka mai sashe 25 sannan sai ya shiga tashar CBT don samun damar amsa tambayoyin da zasu biyo , daga nan ne in yaci, sai ya amshi shaidar tasa.

A cewar sa:

“Ana so mai nema ya ɗauki tsawon mintuna 30 kuma masu neman nasara dole ne su sami damar cin kashi 60% zuwa sama. “Wannan shi ne tabbatacce alamar wucewa wanda zai tabbata da bayar da takaddun tuƙi. Rashin samun wannan makin, sai dai mutum ya sake bayan an buɗe sake rubuta jarabawar kwanaki 7 bayan wannan ta farkon. Inji shi.

Don haka Oyeyemi ya yi kira ga Gwamnatocin Jihohi daban-daban da su hanzarta aiki ta hanyar tabbatar da cewa Hukumomin Ba da lasisin Motocin Jiha sun shiga cikin wannan shiri na ceton rai kamar yadda aka ba Makarantun tuƙi izini don tabbatar da yin aiki kai tsaye.

Shugaban FRSC din ya kuma shawarci Gwamnatocin Jihohi da su tabbatar da cewa CBT ya zama tilas ga duk mai bukata kafin ayi gwajin tuki. Kamar yadda kamfanin dillacin labarai na NAN ya ruwaito.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *