Limanin kha’aba Sheikh Adil Al-Kalbani ya zama jarumin fina-fina.

A wani Rahoto da Islamic Information ta fitar na Cewa Adil Al-Kalbani, tsohon limamin ka’aba, ya gabatar da takaitaccen bayani kan matsayinsa a cikin wani tallan shirin fim na bidiyo Mai Tsawon minti 2 da dakika 41.

Reason Riyadh Kashi na 2021 mai suna ‘Combat Field’ za a gabatar da shi a cikin wani fim na talla wanda ya hada da tsohon Imam Ka’aba Sheikh Adil bin Salem bin Saeed Al-Kalbani da wasu taurarin kwallon kafa.

Bayan

CeCe kuce a shafukan sada zumuntar Zamani masu amfani da shafukan na ci gaba da yi wa tsohon Limanin Ka’aba din Allah wadai tare da fatan shiryar Allah

Sheikh Adil Al-Kabbani ya bayyana ne a cikin wani faifan bidiyo na talla wanda ke nuna yadda sojoji ke yaki da kuma sarrafa makaman yakin. Tsohon Limamin Ka’aban ya yi takaitaccen bayani a cikin faifan bidiyon, wanda ya dauki tsawon mintuna 2 da dakika 41.

Shugaban Hukumar lura da nishadi ta Saudiyya, Turk al-Sheikh ya sanya faifan bidiyon a shafinsa na Twitter, inda tsohon Limamin Ka’aba din sheikh, Adil al-Kalbani cikin barkwanci ya rubuta cewa; “kuna tunanin zan iya zuwa Hollywood?”

Sai dai masu amfani da shafukan sada zumunta din sun caccaki Sheikh Adil Al-Kalbani bayan fitowarsa a faifan bidiyon na tallar. A Lokacin da wani mai amfani da shafukan sada zumunta ya rubuta cewa kasancewar ku a cikin bidiyon baƙon abu ne, sai wani mutum ya amsa masa da cewa, “Allah ya yi muku jagora ya buɗe zuciyar ku.”

Jama’a da dama na kallon Rashin dacewa ga limami Kamar na kha’aba da shiga harkokin fina-fina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *