Mai bawa Ganduje shawara tare dubunnan Mutane sun koma tsagin Shekarau.

Rahotanni daga jihar Kano na Cewa Mohammed Shehu, mai baiwa gwamna Abdullahi Ganduje shawara kan harkokin jihar ya koma jam’iyyar APC karkashin jagorancin Sanata Ibrahim Shekarau a Kano.
Da yake jawabi ga dubban magoya bayan jam’iyyar a karshen mako a Kano, Mista Shehu ya ce ya yanke shawarar shiga sansanin tare da dubban magoya bayansa ne saboda rashin kyakkyawan shugabanci na jam’iyyar da Abdullahi Abbas ke jagoranta.

Mista Shehu ya ce magoya bayansa sun kuduri aniyar yakin neman nasarar Sanata Barau Jibrin a takararsa ta gwamna.

Duk da cewa mafi yawan al’ummar karamar hukumar Nassarawa suna tare da mu, amma shugabannin da Abdullahi Abbas ke jagoranta sun kaurace wa wannan al’amari, suna goyon bayan wasu da ba su da goyon bayan talakawa.

“Bari

in gaya muku cewa ba mu kadai muke cikin wannan tafiya ba. Masu ba da shawara da manyan ’yan siyasa sun fi karkata ga sahihin shugabancin jam’iyyar da Danzago ya samar, kuma muna nan a gida da muradin Sanata Barau Jibrin.

“Sanata Barau Jibrin mutum ne mai gaskiya kuma amintacce wanda kowa ya yarda da shi. Ba a dora shi kan mutanen Kano ba, sai dai su kansu mutanen ne suke son dora shi,” inji shi.

Tun bayan da kotu ta ayyana Haruna Danzago a matsayin sahihin shugabancin jam’iyyar APC, jaridar DAILY NIGERIAN ta samu labarin cewa wasu da dama daga cikin magoya bayan gwamnan sun fara kafa tantunan siyasa a sansanin Shekarau.

Daga cikin wadanda suka yi watsi da Mista Ganduje kwanan nan akwai tsohon mataimakinsa, Hafiz Abubakar da kuma daya daga cikin makusantan sa, Murtala Zainawa.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *