Manya-Manyan labarai guda goma da suka ja hankalin mutane a ƙarshen mako.

1. ‘Yan sanda a Abuja, a jiya, sun ce babu kanshin gaskiya a cikin rahotannin da ke zagayawa cewa Babban Birnin Tarayya yana karkashin mamayar’ yan ta’adda. Kwamishinan ‘yan sanda na Babban birnin tarayyar, Bala Ciroma ya ce’ yan sanda, sojoji da sauran jami’an tsaro na aiki tukuru don tabbatar da lafiyar mazauna garin.

2. Gwamnatin jihar Ondo ta dawo da mutane hamsin da biyu da suka fito daga kasar Hausa wadanda suka dawo jihar daga arewa. Kwamandan rundunar Amotekun, Mista Adetunji Adeleye, ya ce mutanen sun yi ikirarin cewa sun zo ne domin samun horo kan tsaro a wani kamfani mai zaman kansa a jihar.

class="has-text-align-justify">3. Tsohon shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Cif Nnia Nwodo, a jiya, ya ja hankalin masu ruwa da tsaki game da wani shiri na kai masa hari da sunan cewa ya ba na’am da maharan IPOB dake kai hari kan kayan gwamnati da masu zaman kansu a Kudu maso Gabas. Ya yi zargin cewa kungiyar IPOB ta kammala wani shiri na kai harin.

4. Sanannen malamin addinin Kirista na “Adoration Ministry Enugu Nigeria” (AMEN), Rabaran Ejike Mbaka, a jiya yayi watsi zargin da Gwamnatin Tarayya tayi masa na cewa kiran da yayi na a tsige shugaban ƙasa Muhammadu Buhari saboda an hana shi kwangila ne, Mbaka ya ce zargin na yara ne.

5. Biyo bayan ƙaruwar yawan mace-mace da annobar COVID-19 ta haifar a Indiya, Brazil da Turkiya, Gwamnatin Tarayya, a jiya, ta hana matafiya daga ƙasashen uku shiga Najeriya. Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) kuma Shugaban kwamitin Shugabancin (PSC), kan COVID-19, Boss Mustapha ya bayyana hakan a Abuja ranar Lahadi.

6. Hukumar jami’an tsaro ta farin kaya wato (DSS) ta yi gargaɗi ga masu aikata laifuka da ke barazana ga haɗin kan Najeriya da kuma zaman lafiya. Peter Afunanya, mai magana da yawun DSS ɗin ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi.

7. Wasu ƴan bindiga ɗauke da muggan makamai, a jiya, sun kai hari ofishin’ ƴan sanda na Abaomege da ke ƙaramar hukumar Onicha ta jihar Ebonyi. Kwamishinan tsaron cikin gida na Ebonyi, Mista Stanley Okoro-Emegha, ya tabbatar da harin a ranar Lahadi.

8. Jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, a jiya, ya gargadi wadanda ke neman ballewa da su sauya tunanin, inda ya ƙara da cewa ƙasar ba ta gama murmurewa ba daga yaƙin basasa na 1967 – 1970. Tinubu ya yi magana ne a gidan Gwamnatin jihar Lagos da ke Marina yayin wani Tafsirin Ramadan (lacca) wanda Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya shirya.

9. ‘Yan asalin yankin Biafra, IPOB, sun ba da umarnin rufe yankin Kudu maso Gabas, Abuja, Jihar Legas da Arewa a ranar 30 ga Mayu.

10. Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kame wasu kayayaki na kimanin Naira miliyan 170, da ɗigo 7, ciki har da ruwan kwalba, a sashin kula da aiyukan gwamnatin tarayya (FOU) da ke Kaduna da kuma yankin Kirikiri “Lighter Terminal Area” da ke Legas. Kwanturola Albashir Hamisu, ya bayyana hakan yayin wani taron kara wa juna sani a jiya.

Ko wanne ne yafi yan hankalin ka?

Bayyana ra’ayinka.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *