Mata zasu iya tuka nahiyar Africa zuwa matakin Zaman lafiya ~Cewar Shugaba Buhari.

Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), a yau ranar Litinin, ya ce mata za su iya tafiyar da tsarin zaman lafiya wanda a cewarsa ya zama wani batu da ba a taba ganin irinsa ba wanda ke shafar ci gaba a yankuna da dama na Afirka.

Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da yake yin alkawarin ba da goyon baya ga kudurorin zaman lafiya na matan shugabannin Afirka da ke da nufin samar da zaman lafiya da ci gaba a nahiyar.

Mai

ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Litinin.

Sanarwar ta ce Buhari ya kuma bukaci shugabannin Afirka da sauran masu ruwa da tsaki da su mara wa matan baya wajen cimma babban burinsu na gina al’umma mai zaman lafiya.

“Ayyukan ‘yan tada kayar baya da ‘yan bindiga sun haifar da yawaitar tarwatsa jama’a da samar talauci.

“Babu shakka mata da kananan yara ne suka fi fama da tabarbarewar zaman lafiya. Saboda haka, a matsayin iyaye mata, na yi imani, kuna da wani Matsayi na musamman domin fitar da hanyoyin zaman lafiya da ayyuka a inda ya cancanta.

Shugaban ya taya uwargidansa, uwargidan shugaban kasa, Dr Aisha Buhari murnar samun damar jagorancin dukkan matan shugaban kasa domin bunkasa Zaman lafiya a Africa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *