Matashi na matasa Garkuwan matasa Gwamna Yahaya bello ya inganta rayuwar sana’ar matashi.

‘Yan Nijeriya musamman matasa sun yabawa Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello bayan da ya azurta wani matashi mai sana’ar zane-zane da ya zana Gwamnan ya wallafa a Instagram kuma aka yi sa’a Gwamnan ya gani har ma ya yi masa “coment”

Matashin mai mai sunan IG Cridarts ya wallafa zanen hoto Gwamnan inda nan take Gwamnan ya gani yayi masa martani cewa ya ‘zanen ya burgeshi’ kuma zai inganta masa sana’arsa ‘yi mani sako wato DM’ inji Yahaya Bello

Muryoyi

ta ruwaito Galibin wadanda suka bayyana ra’ayinsu akan abunda yayi sun ji dadi domin hakan ya nunawa duniya cewa Gwamnatin mai hulda da kafafen yada labarai na zamani ne kuma hakan ya nuna yana tare da matasa a kodayaushe zai share masu kukansu

“Mafi yawan shuwagabanni a yanzu basa hawa kafafen yada labarai don haka basu san ma halin da kasarsu da al’ummar su ke ciki sai abunda mukarrabansu suka gadama suka nuna masu” wannan ya jawo komi yana tabarbarewa domin shugaba bai ma san me ake ciki ba sai abunda aka zaba aka nuna masa.

Wani mai sharhi kan siyasa Muhammad Muhammad ya ce bincike ya nuna masu a yanzu haka akwai shugaban da buga masa jaridarsa akeyi ta musamman akai masa don haka hadimansa suna zabar abunda suke so a wallafa sannan su kai masa jaridun “sai abunda aka gadama zai sani”

Amma wannan Gwamna ya burge mu domin ya nuna shi matashi ne na matasa kuma yana tare da matasa a kodayaushe

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *