MATSALAR TSARO: Ana kashe mu a kullum don allah gwamnatin Buhari ku dawo mana dashi ~A kudancin Nageriya inyamurai da yarabawa na kukan rashin DCP Abba kyari.

A dai-dai Lokacin da ‘yan kudancin Nageriya ke koke-koke tare da nuna kewarsu ga rashin DCP Abba kyari shi kuwa Shahararran marubucin nan daga kudu maso yammacin Nageriya wato Jihar lagos George Udom Ya fito Fili ya Kuma bukaci Gwamnatin Nageriya Kan ta dawo da DCP Abba kyari Bakin aikinsa Sakamakon tabarbarewar harkokin tsaro daya ta’azzara yankin na Kudancin Nageriya yayi wannan magana ne a shafinsa na Facebook inda ya rubuta cikin harshen turanci amma ga Fassara a harshen hausa Yana Mai cewa dakatar da gogaggen jarumin ‘dan Sanda DCP Abba Kyari ka iya zama barazanar ga Kudu maso Gabashin Nageriya.

Ya

Kuma Kara da Cewa shi wan’can wanda ya maye gurbin Abba kyari Menene sunansa? Kuma yaushe ne za mu fara ganin ayyukansa ko Kuma yana ci gaba da Aikin a Halin yanzu haka?

Wani shima Mai suna Chinedum Agwaramgbo Dan Jihar Enugu Yace Dan Allah yakamata a sake kaddamar da ABBA KYARI!
Domin Ni Ban damu ba a yanzu game da zarge -zargen da ake yi masa … wanda a ainihi sun Kasance zarge -zarge ne marasa tushe!

A Halin Yanzu Kudu Maso Gabas na cikin hadari wanda Yakamata a kawo Mana dauki.

KU DAWO DA ABBA KYARI!

Sai wani sako ta WhatsApp Yana Mai Cewa shin Don Allah za a iya maido da Abba Kyari cikin Rundunar ‘yan sandan Najeriya?

Ya Kara da Cewa Munana tare muggan laifuka da ake aikatawa ba tare da ana hukunta su ba a Kudu maso Gabas abin tsoro ne kuma yana bukatar kulawarsa.

A bisa ra’ayi na Mutumin dake Jagorancin tawagar shi kansa a halin yanzu Yana bukatar dauki ta Hanyar saka takalman Abba kyari domin kaiwa gaci.

Tabbas Yankin Kudu maso Gabas a halin yanzu yana shiga yanayin Gazawa.

Ubangiji ya Tsare Mana Yankinmu na gado.

Wannan ka’dan kenan daga baku nan matasa kudancin Nageriya dake nuna damuwarsu Kan Rashin DCP Abba kyari da tawagar sa idan baku manta ba dai mataimakin Kwamishinan ‘yan Sandan DCP Abba kyari shine Shugaban tawagar Dake fasa gungun membobin ‘yan ta’addan Kungiyar IPOB tare da kawar da gungun masu garkuwa da Mutane a kudancin na Nageriya dama Sauran sassan Nageriya Hakan yasa ma a shekara ta 2020 ne ‘yan majalisar wakilan Nageriya Suka karrama ‘dcp Abba kyarin da Lambar yabo amatsayin gwarzon ‘dan sandan Nageriya…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *