Matsalar Tsaro: Karku sake talakawa su tunzura su tashi a bacci ~Cewa Rahma sadau

Batun Matsalar Rashin tsaro jarumar Kannywood, Rahama Sadau, ta yi tsokaci kan matsalar rashin tsaro da ake fama dashi musamman a arewacin kasar.

A wani sako da ta wallafa a shafinta na sada zumunta, jarumar ta ce kawo ‘yan kasar ba su tabuka wani abin da ya dace kan wannan zalunci ba.
Sadau ta ce talaka ba shi da Zaman lafiya ko da kuwa a kusurwar gidansa hudu.

Sai dai ta yi kira ga daukacin ‘yan Najeriya masu murya, ko mulki ko kuma masu fada a ji da su hada kai don yakar tabarbarewar tsaro da ke mayar da kasar nan tamkar filin kashe-kashe.

Sadau

ta rubuta cewa, “Hotunan da suka tayar da hankali na kwanan nan a shafukan sada zumunta suna da ban takaici da rashin mutuntaka. Me muka yi a matsayinmu na ’yan kasa (Arewa musamman) da muka cancanci irin wannan zalunci da rashin kulawa daga shugabanninmu?? Duk abin da muka yi shi ne ZABE!!

“Yaushe za a dauki mataki kan rashin tsaro???Yaushe za a ji muryoyin mu??? Ana lura da hankalinmu ne kawai bayan kowace shekara 4… to YA isa haka!!

“Wannan rashin tsaro yakasance yana shafar KOWANNE gida a Arewa…… Hmm!! Kada Ku Tashe talaka a Barci… Talaka a yau, zama a cikin gidansa ma tsoro yake bashi.

“Ina kira ga kowa da kowa da murya, iko da tasiri da su ba da gudummawa wajen magance rashin tsaro a Najeriya. Satar AREWA ga ‘yan fashi kamar zaluntar al’umma ne. Idan kowa ya mutu Sai muga wanda zai zabe su Babu wani Mai Zama lafiya.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *