Matsalar tsaro tazo Karshe a Nageriya Lokaci ka’dan ya rage ~Cewar Osinbanjo.

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya tabbatar da cewa za a magance matsalolin tsaro da suka dabaibaye kasar nan bada jumawa.

Wannan kamar yadda ya ce bai kamata ‘yan Najeriya su yi kasa a gwiwa ba wajen kiyaye manufofin kasar kuma kada su manta da abin da suke kokarin cimmawa na magance Matsalar tsaro.

Osinbajo ya bayyana haka ne a ranar Alhamis yayin da ya karbi bakuncin kungiyar Muhammadu Buhari Dynamic Support Group, a fadar shugaban kasa ta Villa.

Babban

mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban kasa kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Laolu Akande, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa mai taken, ‘VP harps on unity as Buhari/Osinbajo Support Groups ya yabawa “fificinsa, tawali’u da sadaukar da kai ga aikin

A cewarsa, “Yawancin matsalolin tsaro da muke gani a yau, idan lokaci ya yi, za a magance su, kuma kasar nan za ta kara karfi sosai.

“Bai kamata mu yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da cewa mun ci gaba da bin manufofin kasar nan kuma kada mu manta da abin da muke kokarin cimmawa a nan.

“Shugaban kasa a koda yaushe ya tsaya tsayin daka yana mai da hankali wajen magance matsalolin kasar Nan ba tare da ya jin tsoro ba, ba ya firgita, yana mai da hankali da duba al’amuran tsaro a kowacce rana, yana kokarin ganin ci gaba da mafi kyawun mafita, Inji Mataimakin Shugaban

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *