Milyan daya da rabi 1.5m muke karba amatsayin albashi duk wata ~Cewar Sanata Ahmad lawan.

Shugaban Majalisar Dattawan Nageriya Dakta Ahmad Lawan, ya bayyana albashin ‘yan majalisar tarayya da kudaden alawus-alawus, inda ya ce Sanata na karbar Naira miliyan 1.5 duk wata yayin da dan majalisar ke karbar Naira miliyan 1.3 a matsayin albashi.

Lawan, wanda ya bayyana hakan a Abuja ranar Litinin a wajen taron lacca na ‘yan majalisar wakilai na farko da cibiyar nazarin harkokin dokoki da dimokuradiyya ta kasa ta shirya, ya ce Naira miliyan 13 da aka yadawa jama’a a shekarun baya amatsayin albashin da Sanata ke karba a duk wata shi ne ainihin alawus na gudanar da ofis.

Kalaman

sa: “Jimillar albashin dan majalisar dattawa ya kai kusan N1.5m yayin da na majalisar wakilai ya kai kusan N1.3m.

“Kudin da ake ba wa ‘yan majalisar alawus na ofis a duk wata shi ne abin da ke cin karo da kuskure da kudaden shiga na wata-wata don haifar da rudani da yaudarar ‘yan Najeriya.

“Matsakaicin kudin ofis na sanata kusan N13m yayin da dan majalisar wakilai ya kai N8m.”
Lawan ya jaddada cewa N13m da N8m na gudanar da ofis a duk wata kwata-kwata ga dan majalisar dattawa da ta wakilai, su ne mafi karanci a duk wata kasar dimokuradiyyar shugaban kasa a duniya.

A cewarsa, alawus-alawus din sun hada da kudaden da ake kashewa na balaguron gida/na kasa da kasa, tuntubar kwararrun ma’aikata, ayyukan likitanci, kayayyakin ofis/kwamfutoci, kayan masarufi, litattafai, jaridu, mujallu, kula da motoci da kayayyakin ofis, da dai sauransu.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *