Ministan Tsaro ɗauke da bindinga ƙirar Ak47 yana shiga Mota, zai gama bayyana maka yadda ƙasa ta shiga halin laila-ha-ula-i.

Zuwa yanzu, dukkan mu mun gaji da samun labarai kan yawan kai hare-hare da sace-sacen mutane.

Matsalar tsaro a Najeriya na ci gaba da taɓarɓarewa kowacce rana.

Ga ƴan arewa, rikicin Boko Haram ne, kuma a halin yanzu Kudu maso Gabas na yaƙi da fama da ƴan bindiga da ba’a san su ba ne.

To sai dai yayin da ake fama da waɗannan kalubalen tsaro an hango wani faifan bidiyo na baya-bayan nan, wnada ke ɗauke da ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi (mai ritaya) ɗauke da makami samfurin AK47 bindinga yayin da yake shiga motarsa sanye da kayan gida.

class="wp-block-image size-full">

Sai dai abin da ya ja hankali shi ne yadda aka ga ministan yana ɗauke da bindiga yayin da ya shiga motarsa, wanda ba’a cika ganin babban mutum yayi haka ba.

Duk da a yan kwanakin nan ana samun cigaba a harkar tsaro, kuma abin yana daɗi sosai, amma abune mai ban mamaki ace yanayin tsaro a ƙasar nan har takai ministan tsaro da saɓa bindinga kamar ɗan sanda?

Ku yi tunanin ministan tsaro yana ɗauke da bindiga da kansa, yayin da yake shirin fita, saboda bai san abin da zai iya jiran sa a kan hanya ba, ina kuma ga Ni da kai mai neman na kaiwa bakin salati???

Ya kamata ace kowa ya soma ɗaukan matakin kare kansa kamar yadda minista yayi, koda kuwa ba makami irin nasa za’a riƙe ba.

Menene tunanin ku akan haka?

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *