Mu a jihar Kano Bola Tinubu zamu bawa ƙuri’un mu a zaben 2023 Mai zuwa ~Cewar Gwamnatin Kano.

Shugaban majalisar dokokin Kano, Hamisu Chidari ya bayyana cewa jiharsa za ta marawa Bola Tinubu, tsohon gwamnan Legas goyon baya a matsayin shugaban kasa a 2023.

Chidari yayin da yake jawabi a wajen kaddamar da kungiyar goyon bayan Tinubu (TSG) da kwamitocin gudanarwa na kungiyar a Abuja ranar Asabar, ya ce Kano za ta bai wa Tinubu kuri’u a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC.
A cewar shugaban majalisar, yankin arewa maso yamma na sane da irin rawar da tsohon gwamnan Legas ya taka wajen ganin an zabi shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2015.

“Manufana

ita ce in fara tafiyar da za ta kai mu Villa da yardar Allah tare da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin na daya daga cikin ‘yan Najeriya,” inji shi.

“A Kano, kasancewar jihar da ke da yawan wakilai, mun riga mun yanke shawara kuma mun riga mun kammala; za mu ba shi akalla kashi 98 na wakilai a zaben fidda gwani.

Ba wannan kadai ba, mu ne za mu ba shi mafi yawan kuri’u domin a ranar 29 ga Mayu, 2023, Haka Kuma za mu kasance a dandalin Eagle Square domin rantsar da shi a matsayin shugaban kasa.

“Dukkanmu ‘yan arewa maso yamma muna sane da irin rawar da ya taka wajen kai danmu shugaban kasa Muhammadu Buhari fadar Villa. Don haka, za mu ba shi lada; za mu mayar masa.

Don haka, na tabbatar masa da nasara. Kusan dukkan wakilai daga jihohin arewa maso yamma ne za su zabe shi a zaben fidda gwani na gaba.”

Kawo yanzu dai Tinubu bai bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 ba Haka Kuma Ganduje na Daya daga Cikin Jerin Gwamnoni dake goyon bayan Bola Ahmad Tinubu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *