Mun karbi mulki Cikin Matsalar ta’addanci amma zamu mika Mulki ga wasu bayan mun kawo karshen ta’addancin ~Cewar Masari.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari ya ce gwamnatinsa za ta yi amfani da mutane da fasaha Zamani wajen fatattakar ‘yan bindiga da ke addabar Katsina.

Gwamnan wanda ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai a ranar Talata a Katsina, ya bukaci mazauna yankin da su yi iya kokarinsu wajen kare yankunansu daga hare-haren ‘yan bindiga.

Ya kara da cewa “mun gaji gwamnati ne da matsalolin tsaro kuma dole ne mu kawo karshenta mu mika jihar ga wadanda za su gaje mu ba tare da wannan matsala ba,

A

kwanakin baya ne gwamnatin Katsina ta dage haramcin ayyukan sadarwa a kananan hukumomi 10 cikin 17 da ke cikin kananan hukumomi 17 a sakamakon hare-haren da ‘yan bindiga ke kai wa.

Ya yabawa kokarin dukkan hukumomin tsaro musamman kungiyoyin sa ido kan yaki da ‘yan bindiga.

Masari ya bayyana cewa ’yan banga na tafiya daga wannan al’umma zuwa waccan da nufin kare al’umma.

Gwamnan ya kuma shawarci jama’a da su kare al’ummarsu tare da baiwa jami’an tsaro duk wani tallafi da ya kamata, musamman ta hanyar basu sahihin bayanai kan masu aikata laifuka.

Gwamnan ya bukaci jama’a da su tallafa wa kungiyoyin ‘yan banga da makaman da suka dace domin su kare su idan aka kai musu hari.

A baya gwamnan ya ce dole ne a fatattaki ‘yan fashi baki daya a Arewa kafin shekarar 2023.

Mista Masari, wanda ya ba da tabbacin a lokacin da ya sanya hannu kan kudurin kasafin kudin jihar na shekarar 2022, ya ce babu ja da baya a yakin da ake da ‘yan bindiga.

“Dole ne mu shirya yin yaki, mu yaki ‘yan bindigar saboda mugaye ne kuma suna wakiltar mugaye. Bai kamata mu ja da baya a wannan yaƙin ba. Mun karbi ragamar mulkin kasar ne cikin tsananin barazanar tsaro a shekarar 2015, kuma da yardar Allah ba za mu mika kasar nan ga shugabanni masu zuwa a karkashin wannan yanayi ba. Dole ne mu dawo da zaman lafiya,” in ji Mista Masari.

(NAN)

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *