Mun kashe tiriliyan biyu da ‘digo uku 2.3tr wajen tallafi ga Jama’a a Lokaci Corona Virus ~Cewar Gwamnatin Shugaba Buhari.

A wani taro da ya halarta Karamin Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare na Kasa, Prince Clem Agba ya ce Gwamnatin Tarayya ta kashe sama da Naira Tiriliyan 2.3 a matsayin wani kunshin tallafi don dakile illolin annobar COVID-19.

Agba ya bayyana hakan ne a jiya ranar Talata a wajen taron karawa juna sani na kwana 3 na baitul malin kasa mai taken: ‘Covid-19 and the world Economic: Implications on Nigeria’s National Treasury,’ wanda ofishin Akanta Janar na kasa ya shirya wanda aka gudanar a Uyo. Babban birnin jihar Akwa Ibom.

Ya

ce manufofin kasafin kudi da hada-hadar kudi sune tallafi ga jihohi, ‘yan kasuwa da gidaje da daidaikun jama’a ta hanyar tallafi, rage haraji, tallafin albashi, tare da tallafin kai tsaye ga bangaren lafiya.

A cewar ministan sun fi mayar da hankali ne kan noma da Samar da gidaje ga jama’a, da ayyukan jama’a, na’urori masu amfani da hasken rana da kuma tallafawa kananan ‘yan kasuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *