Mun kwato Bilyan 19.3bn da Gwamnatin jihar kogi ta boye a bankin Starling mun kuma koma dasu CBN ~Cewar Hukumar EFCC.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta ce ta mayar da kudade Naira biliyan 19.3 da aka ce gwamnatin jihar Kogi ta boye zuwa babban bankin Najeriya (CBN).

A baya dai hukumar ta bayyana cewa gwamnatin Gwamna Yahaya Bello ta boye kudaden ne a wani asusun ajiyar banki na Sterling.

Gwamnatin jihar Kogi dai ta musanta boye kudaden, inda ta zargi hukumar EFCC da tabka magudi da sharri.

Sai

dai a wata sanarwa a ranar Juma’a, mai magana da yawun hukumar Wilson Uwujaren, ya ce an tura kudaden zuwa babban bankin Nageriya bayan an kwato su.

“Babban bankin Najeriya, CBN, ya amince da karbar kudi Bilyan N19, 333,333,333.36 (Biliyan sha tara da miliyan dari uku da talatin da uku, dubu dari uku da talatin da uku, dari uku da talatin da uku, naira talatin- shida Kobo) wanda EFCC ta kwato daga asusun belin albashi na jihar Kogi dake zaune a bankin Sterling Bank Plc. Wannan ya sanya ya dakatar da yakin neman zabe na karya da kuma karyata rashin fahimta da gwamnatin jihar Kogi ta yi cewa ba a kwato wani asusu daga asusun na ta ba

“Babban bankin a cikin wata wasika mai lamba DFD/DIR/CON/EXT/01/099 ranar 9 ga Nuwamba, 2021 ya sanar da Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa cewa ya karbi kudin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *