Muna Allah wadai da harin ta’addancin da aka kaiwa Sanata danjuma goje ~Cewar Kungiyar Izalah.

A Jiya Ranar Asabar a wani jawabi daya wallafa ba shafin sa na Facebook Mohammed Adamu yayari Mai hidimtawa Sanata danjuma goje Kan kafafen sada zumuntar Zamani Yana Mai Cewa Malaman Addini sunyi Allah wadai da abunda aka yiwa Sanata Danjuma Goje jiya akan hanyarsa na shigowa Gombe.

Jagoran siyasar jihar Gombe Sanata Muhammad Danjuma Goje, A yau ya karbi bakwancin shuwagabannin kungiyoyar Jama’atul izalatul bidi’a wa’ikamatu Sunnah bagaren Jos da Kaduna da kuma shuwagabannin kungiyar fitiyanul Islam na kananan hukumomin Akko da Yamaltu Deba.

Shuwagabannin

Kungiyoyin sun kawo ziyara ga Sanata Goje ne don Mika godiyarsu dangane da kyautar motoci guda 6 wadda Sanata Goje ya yiwa bangarorin kungiyoyin gaba daya na kananan hukumomin Akko da Yamaltu Deba.

Alaramma Mujahid Sheik Ibrahim Baure wanda yayi godiya amadadin Alarammomi da kungiyar Fitiyanul Islam na karamar hukumar Yamaltu Deba yace kafun godiya Suna jajantawa Sanata akan abunda ya faru da shi jiya, kuma yana tabbatarwa sanata cewa duka Allaramomi basu ji dadin abunda ya faru dashi ba.

Shima a jawabinsa na godiya shugaban kungiyar Jama’atul izalatul bidi’a wa ikamatus sunnah mai helkwata a Jos na karamar Hukumar Akko, Sheikh Seyoji muhammad yace a wakilci da Sanata yake yi sun ga alherai iri-iri wadda suka haďa da gina masallaci, ba su zakka da kuma kyautar mota. don haka suna godiya akan kokari da Sanata Yake musu.

Da yake godiya ga shuwagabannin kungiyoyin da suka ziyarce shi, Sanata Goje ya shaida musu cewa zai cigaba da tallafawa harkokin addini har karshen rayuwarsa, ya kuma yi kira gare su da su cigaba da addu’o’in neman zaman lafiya wa jihar Gombe da Nigeria baki daya. Muhammad Adamu Yayari,
New Media aide to
Sen. Danjuma Goje
Sat, 6 Nov 2021.

Idan baku manta ba a Ranar juma’a data gabata ne wasu gungun matasa ‘yan Daba dauke da muggan makamai Suka tare Hanyar Sanata danjuma goje a Lokacin daya ke kokarin Shiga Garin Gombe domin halartar daurin Lamarin da yayi sanadiyar kone-konen tayoyin mota da Sauran su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *