Muna bawa Sanatocin arewacin Nageriya shawara da suyi koyi da Sanata Uba sani wajen inganta rayuwar matasa.

Da’ace Sanatocin arewacin Nageriya zasu mai da Hankali Kamar yadda Sanata Uba sani ke kokari a fanni da dama domin kawo karshen zaman Banza tabbas da an samu sauƙin lamura musamman Matsalar Rashin tsaro talauci da rashin ilmi da ake fama dasu a wannan yanki namu mai albarka na arewacin Nageriya.

Sanata Uba sani shine ‘dan majalisar dattijan Nageriya dake wakiltar kaduna ta tsakiya a majalisar dattijan Nageriya daga 2019 zuwa Yanzu.

Sanata Uba sani a Lokacin da yake yakin Neman a zabe shi ya tabbatar da Cewa shi ba don neman kudi zai nemi kujerar zama Sanata ba domin duk wata irin nau’in Ni’ima da yake nema Allah ya bashi don Haka ya zo majalisar ne domin ya taimaki Al’ummar yankinsa da kaduna dama Nageriya gaba ‘daya.

Duba

da Matsalar dake faruwa na shigar matasa harkokin ta’addanci a Nageriya da Kuma Kasancewar Bincike ya tabbatar da Cewa Yunwa , Jahilci, da rashin aikinyi sune Manyan Manyan dalilan dake saka matasa shiga harkokin ta’addanci Sanata Uba sani yayi anfani da wannan damar daya samu a majalisar dattijan Nageriya amatsayin sa na Shugaban kwamitin Bankuna Inshora da Sauran Harkokin Ku’di wajen ganin ya samar da ayyukan yi ga matasa.

Ya Samar da jari milyoyin Ku’di ga dubban matasa tare da koya masu sana’o’i kala-kala domin kawo karshen zaman Banza.

Ya samar da cibiyoyin koyon na’ura Mai kwakwalwa domin tabbatar rayuwa Mai kyau ga matasan.

A jiharsa ta kaduna Ya Kai kudri an kafa jami’o’i da dama tare da gyaran wasu Makarantu domin ingantuwar ilmin matasan a kokarin sa na yaki da Jahilci.

Sanata Uba sani sune suka zauna Suka kuma tsara Suka kafa tsarin bayarda rance ga ‘yan Nageriya masu kananan sana’a domin inganta rayuwar matasan ta gobe.

Hakan shine Shugabancin da muke bukata Yanzu ace dukkan Sanatocin mu na arewa suna ire iren wannan kokari na Sanata Uba sani to ta Ina za”a samu Matsalar Rashin tsaro Jahilci da Zaman banza?

Muna Kira ga ‘yan majalisar dattijan Nageriya Dana wakilai da suyi koyi da Sanata Uba sani a fagen yaki da talauci Rashin sana’a da Rashin Ilimi ga matasa domin kawo Karshen ta’addanci da ake fama dashi a Nageriya musamman Yankin mu na arewa. ~rubutawa Jamila Bashir Ahmad.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *