Muna ciyarda talakawa mutun milyan tara 9m zamu Kara mutun milyan biyar 5m a Shirin mu na ciyarwa ~Cewar ministan Jin Kai Sadiya Farouq

Ministar kula da jin kai da ci gaban jama’a, Hajiya Sadiya Umar ta ce sama da dalibai miliyan tara ne suka amfana da shirin ciyar da makarantu na gida gida (NHGSFP).

Sadiya ta bayyana haka ne a ranar Talata a Makurdi a wajen bikin mika kayan girki ga makarantar firamare ta karamar hukumar (LGEA) da ke Wurukum.

Ministan wanda ta samu wakilcin mataimakin daraktan gudanarwa na gwamnati, Mista Ladan Haruna, ya ce an yi shirin NHGSFP ne domin fitar da ‘yan Najeriya daga kangin talauci.

Ta

ce sama da masu dafa abinci 100,000 ne suka tsunduma cikin shirin a fadin kasar.

A cewarta, shirin, wani shiri ne na hadin gwiwa da gwamnatin tarayya, na kokarin inganta karatun dalibai, da inganta darajar abinci mai gina jiki da kuma tasiri ga tattalin arzikin kananan hukumomi.

Ta kuma ce shirin ya samar da ayyukan yi a cikin tsarin ciyar da makarantu a bangarorin sufuri da masana’antu.

Ta yi bayanin cewa ma’aikatar ta gano wuraren da za a inganta don bunkasa shirin tare da karin masu cin gajiyar har mutun miliyan biyar.

A cewarta, wasu daga cikin wuraren da aka gano sun hada da atisayen kidayar jama’a a fadin kasar da manufar tantance bayanai, da inganta ingancin bayanai da sabunta bayanan da ake da su domin daukar aikin tantancewar.

Ta kuma ce za a sake duba shirin domin ganin ya cika manufofinsa.
Sadiya ta tabbatar wa al’umma cewa ma’aikatar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen samar da ayyukan yi.

Da yake karbar kayayyakin, Gwamna Samuel Ortom na Benuwe wanda sakataren gwamnatin jihar ya wakilta, Farfesa Tony Ijohor, ya ce gwamnatinsa ta kuma horar da masu dafa abinci kan kiwon lafiya da tsafta da ka’idojin COVID-19.

Ya ce horon ya kara habaka karfin masu dafa abinci wajen gudanar da ayyuka tare da dakile yaduwar cututtuka.

Gwamnan ya yi alkawarin tallafawa gwamnatin tarayya wajen aiwatar da shirye-shiryenta na zuba jari na kasa don fitar da ‘yan Najeriya daga kangin talauci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *