Muna rokon Buhari ya saka dokar hana cin Kare a Najeriya |– Inji Natasha Choolun

Wata mai rajin kare dabbobi, mazauniyar kasar Birtaniya Natasha Choolun ta bayyana cewa akalla mutum 10,000 ne suka saka hannu a kira da a saka dokar hana cin kare a Najeriya.

Kare nama ne da ke da daraja musamman a yankin kudancin Najeriya musamman jihohin kudu maso gabas da jihohin Akwa Ibom da Cross Rivers.

Mutanen wannan yanki na daraja naman kare musamman idan aka zo shan giyar Kai-kai inda ake hada naman da ƴar wata ganye mai ƙamshin da ke sa mashaya na cin duniyar su da tsinke.

Choolun

ta ce ya kamata Buhari ya saka doka da zai hana mutane cin kare, suma a kare su.

” Yanzu fa masu kiwon kare da ajiye karnuka suna cikin fargaba domin idan mutum ya kau ido sai ya nemi karensa ya rasa.

Sannan kuma maimakon kiwo da amfani da su a matsayin abokan zama, safarar su ake yi kasashe kasashe ana sai da su domin a rangaɗa farfesu dasu.

Akalla mutane 10,000 ne suka saka hannu a wannan kira na hana cin kare a Najeriya wanda aka yi shi a yanar gizo.

Bisa haka ne kuma suke kira ga shugaban kasa Buhari ya saka dokar da za ta hana cin kare a kasar nan.

Daga: Ahmad Aminu Kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *