Na bawa Gwamnatin Tarayya shawara da dabarun yadda za’a kawo karshen Kashe Kashe da zubda jini ~Cewar Shakarau.

A wata sanarwa da ya fitar domin aikewa da Sakon ta’aziyya da jimami Kan Kashe Kashen Nageriya Sanata Malam Ibrahim Shekarau ya na Mai Cewa

HASBUNALLAHU WA NIIMAL WAKEEL

Assalamu alaikum

A kwanaki shida da suka gabata na yi takakkiya har zuwa garin Badau na karamar hukumar Bagwai ta jihar Kano domin yin ta’aziyya na mutuwar mutum 40 sakamakon hadarin jirgin ruwa. Wannan rashi da labarin yadda ya faru ya abin tashin hankali ne. Kada Allah ya maimaita mana ganin irin wannan musiba.

Shekara

jiya kuma, a Sabon Birni na jihar Sokoto ‘yan ta’adda suka bankawa motar fasinja wuta. Mutanen cikin kusan 42 suka kone, an yi janaizar mutum 30, yara da mata da jarirai suka halaka. Al’amarin nan ya munana.

Allah ga mu gareka. Allah mun tuba. Allah ka kawo mana dauki daga gareka.

Akalla shekara biyu da suka gabata a matsayina na wakilin mutanen Kano Central a majalisar dattijai, na gabatarwa da gwamnatinmu shawarwari da dabaru da zamu hada karfi da karfe na yadda za a shawo kan wannan zub da jini da asarar rayuka, kuma har yau ban gajiya ba, zan ci gaba da bi har Allah ya datar damu.

Ina amfani da wannan dama na mika sakon ta’aziyya ga gwamnatin jihar Kano da gwamnatin jihar Sakkwato da iyalin duk wanda wannan musiba ta shafa da sauran al’ummar Najeriya, Allah ya jikan mamatanmu, Allah ya karbi shahadarsu.

Wadannan miyagu kuma zamu ci gaba da yi musu addua, Allah ya yi mana maganinsu. Allah ya lalata aniyarsu. Allah ya kawo mana karshensu.

Nagode

-MIS

Sanata Ibrahim Shekarau
Sardaunan Kano

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *