Na cire rai da Sheƙau domin ya jefa ni cikin ƙunci, ni da shi Shari’a sai a lahira |~ Inji Mahaifiyar Sheƙau

Fatima Abubakar, mahaifiyar tsohon shugaban kungiyar ta’addanci ta Boko Haram, Abubakar Shekau, ta ce bata da masaniya ko danta yana da yara.

Fatima, wacce ta bayana hakan a wani hira da ta yi da Trust TV, ta ce ko yana raye ko mace, babu wani abu da ke tsakaninta da shi.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Fatima ta bayyana cewa Shekau ya jefa ta cikin ukuba har ta kai cewa ta cire rai da shi.

Ta

ce: “A bangare na, ni na tsuguna na haifi shi, wannan shine abin da kadai ke tsakanin mu. Ko yana da rai ko ya mutu; mun raba jiha.

“Ban taba sanin ko yana da ‘ya’ya ba ko kuma ba shi da su.

Ya jefa ni cikin bakin ciki. Allah zai yi hisabi tsakanin mu a ranar gobe kiyama.”

A watan Mayun shekarar 2021, an kashe Shekau yayin fada tsakaninsa da mayakin kungiyar Islamic State in West Africa Province (ISWAP).

Rahotanni sun ce ya halaka kansa a yayin da ya lura mayakan na ISWAP na daf da cin masa da ransa.

Daga Ahmad Aminu Kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *