Na kaiwa Al’umma ta Ayyukan Bilyan biyar Cikin Shekaru biyu a Tarihin Jihar kaduna ba’a tabayin Sanata Irina ba ~Inji Sanata Uba Sani.

A wata bibiya da Jaridar Mikiya tayi Cikin wata fira da Gidan radion Freedom tayi da Sanatan jiya Asabar da misalin karfe 08:30 na dare Sanata Malam Uba Sani wakilin kaduna ta tsakiya a majalisar dattijan Nageriya Malam uba sani ya bayyana kadan daga Cikin irin kokari tare da aikin Alkharin daya kai wa Al’ummar da yake wakilta tun Bayan zuwansa majalisar Tsawon Shekaru biyu.

inda Sanatan ya bugi kirji Yana Mai Cewa A tarihin jihar kaduna tun Bayan kafuwarta a mulkin Dimokuradiyya babu wani Senator da ya tabayin kudurori guda goma sha tara 19 sai ni uba sani

Sanatan

Yace Wanda muke sa rai daya daga cikin kudurorin Shugaba Buhari zai sa masa hannu Kan Kudirin asibitin tarayya (Federal Medical center Rigasa) bayan Majalisar wakilai sun gama mahawara domin tuni majalisar dattijai suka riga suka gama nasu muhawarorin.

Sanatan ya Kara da Cewa kawo yanzu na kawo ma mutanan kaduna ta tsakiya Ayyuka na a kalla sama da Naira Bilyan biyar 5bn acikin shekaru biyu kacal.

Kuma na sanya angina a makatantar kwana dake Kawo cikin garin Kaduna, ICT center wanda aka zuba na’ura Mai kwakwalwa Guda dari biyar 500 duk domin inganta karatun yaranmu.

Idan baku manta ba dai sanata uba sani ya samu lambobin yabo Kan wakilci na Gari ga Al’ummarsa musamman yadda sanatan ya shahara wajen Samar da jari ga matasan Jihar kaduna dama Wasu Dake arewacin Nageriya…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *