Na tabbatarwa da mata samun goyon bayana domin taka kyakkyawar rawa Cikin Jam’iyar APC a zabe mai zuwa ~Cewar Sanata Uba Sani

Sanata Malama Uba Sani dake wakiltar kaduna ta tsakiya a majalisar dattijan Nageriya ya Bayyana mahimmancin zaburar da mata a Cikin Al’umma Sanatan ya Fadi Hakan ne a wani matakin Dalilin taron Mata a Yankin da na kaduna ta tsakiya Sanatan Yana Cewa A ci gaba da tattaunawa ta da masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC a jihar Kaduna, a yau na gana da shugabannin mata a matakin kananan hukumomi da mazabu na shiyyar Kaduna ta tsakiya.

Makasudin

taron suka halarta shi ne domin zaburar da mata, samar da hadin kai a tsakanin su domin taka rawar gani a yakin zabe na APC a nan gaba. Na kuma tabbatar wa matan da goyon bayana gaba daya yayin da suke kokarin yin tasiri ga jam’iyya da tsarin zabe. Na shawarce su da su rika ganin kan su a matsayin abokan hadin gwiwa a harkar gina jam’iyya da ci gaban kasa, su koyi tafiyar da bambance-bambancen da ke tsakaninsu domin maslahar jam’iyya da ci gaban kasarmu.

Matan karkashin jagorancin shugabar matan jihar, Hajiya Maryam Mai Rusau da shugabar mata ta shiyyar (Zone II), Hajiya A’isha Idris sun bayyana kudirinsu na ganin an farfado da reshen mata tare da gudanar Jam’iyar Zuwa ga Nasara a mataki na Gaba.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *