Naira Mai Saka Ango Ya Manta Sunan Amarya: Wasu ƙarata sun ragargaji tsallen baɗake a cikin taɓo saboda feshin kuɗi da wasu matasa a jerin gwanon motoci sukai musu.

Wani faifan bidiyon mai motsi da yake yawo a yanar gizo-gizo ya nuno wasu matasa cikin izza da isa yayin da suka durfafi wani yanki cikin salo irin na isa kai kace ɗan ƙaruna ne yazo yankin.

Matasan sunyi jerin gwanon motoci ne na alfarma, sa’ilin da suke tuƙi cikin gwaninta gamida nuna isa a wani titi mai cike da taɓo, ruwa da kwazazzabai.

Tabbas, duk wanda yaga Faifan bidiyon, zaice kuɗi ga wajen da ake kashe ku.

class="has-text-align-justify">Matasan basu tsaya anan ba, sun durfafi yankin suna watsa kuɗi a sararin samaniya, kai kace yayi da shara suke zubarwa.Ai kam kan kace kwabo, tuni, mutanen yankin suka ce dawa aka haɗa mu idan bada ku ba? Nan take, suka bazamo, jama’a ta haɗu kamar ana suna a gidan mai gari.

Jefa kuɗin da sukeyi ne, yasa aka hango wasu mutanen yankin, nata dadafniya a cikin taɓo suna ƙoƙarin tara kuɗi, saboda yadda matasan ke fesar da kuɗi.

Wa yaƙi kuɗi?

Domin kallon Faifan bidiyon danna nan:

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *