Najeriya Kasa Ce Mai cike da tsananin bakin ciki da bacin rai ~ inji Obasanjo

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana Najeriya a matsayin kasa mai cike da daci da bakin ciki.

Tsohon shugaban kasar a ranar Alhamis din da ta gabata ya ce mummunan shugabanci ya hana kasar cimma nasarorinta.

Ya fadi haka ne a ranar Alhamis yayin da aka gabatar masa da wani littafi mai suna, ‘The Man, The General and the President,’ wanda Femmy Carrena ya rubuta, a dakin karatu na Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta, a babban birnin jihar Ogun.

Obasanjo

ya ce, “Addu’ata ita ce dukkanmu mu sami abin da za mu ba da gudummawa don mayar da kasar nan abin da Allah ya halicce ta ta zama – kasar da ke malala da madara da zuma.

“A yanzu haka, kasa ce da ke ci gaba da daci da bakin ciki, ba haka Allah yake son kasar nan ta kasance ba.

“Dole ne mu canza labari, dole ne muyi magana da kawunanmu cikin yaren wayewa.

“Babu inda ka je a kasar nan da ba za ka ga masu hazaka a kowane sashe na kasar ba.  Don haka, me ya sa za mu raina kanmu? ”
Maryam Gidado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *