Najeriya Zata Zama Kasa Mafi Amincin Rayuwa bil’adama Idan Na Zama Shugaban Kasa A 2023~Cewar Yahaya Bello.

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello a ranar Larabar da ta gabata ya ce zai maimaita duk nasarorin da ya samu a jiharsa a matakin kasa idan ya zama shugaban kasa a 2023.

Da yake magana a cikin shirin gidan Talabijin na Channels ‘Politics Today’ wanda JARIDAR MIKIYA ke sa ido, gwamnan wanda ya bayyana tsaro a matsayin ajanda na daya a kowace kasa ya ce zai sanya Najeriya ta zama kasa mafi aminci kamar yadda jihar Kogi ta kasance jiha mafi aminci a kasar karkashin jagorancin sa.

class="sharedaddy sd-sharing-enabled">

Share this:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *