Nan gaba kaɗan Buhari zai ayyana ƴan fashin daji a matsayin ƴan ta’adda, domin abubuwan da suke aikatawa sun ma fi na ƴan ta’adda – Majalisar Wakila

Majalisar Wakilan Najeriya ta bayyana fatan cewa nan ba da daɗewa ba, Shugaba Muhammadu Buhari zai sa hannu kan ƙudurin da ke neman ayyana ‘yan fashin daji a matsayin ‘yan ta’adda.

Ana dai ta ƙara samun kiraye-kirayen a ɗauki wannan mataki, don ba da dama ga dakarun tsaron ƙasar su kai ƙarin kayan yaƙi da nufin murƙushe ‘yan fashin daji da suka addabi yankunan arewa maso yamma da sassan arewa ta tsakiya.

Sai

dai, a baya-bayan nan wasu rahotanni sun ambato rundunar sojin Najeriya na shaida wa ‘yan majalisar ƙasar cewa suna da tarnaƙi wajen yaƙar ‘yan fashin daji da sabbin jiragen da Najeriya ta sayo daga Amurka wato A-29 Super Tucano guda 12, saboda mai sayarwar ta gindaya sharaɗin cewa ba za a yi amfani da su ba, face wajen yaƙar ‘yan ta’adda da kuma ‘yan ta-da-ƙayar-baya.

Shugaban kwamitin kula da harkokin sojin ƙasa a majalisar wakilan Najeriya Honourable Abdurrazaƙ Namdaz, ya ce dukkanin majalisu wakilai da na dattawa sun amince shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kira ƴan bindiga a matsayin ƴan ta’adda, har ma sun yi ƙuduri sun aika masa, kuma suna kyautata zaton cewa zai amince da wannan bukata”

A cewarsa ”Abubuwan da suke aikatawa sun ma fi na ƴan ta’adda, kana ganin kwanan nan an kashe mutane sun fi 50 a Sokoto, ba za a bar mutanen da suke kashe mutane haka kawai su ci gaba da cin karensu ba babbaka.”

Ya ƙara da cewa ”Kashe-kashe na yawa a ƙasar nan, ana kashe mutane yara da mata, amma sai a yi ta tafiya a kan maganar cewa akwai yancin kare ɗan adam, mun yadda akwai wannan, amma ba zai yi wu a zuba musu ido haka kawai ba”

Masana harkokin tsaro dai sun yi imanin cewa ayyana yan fashin dajin a matsayin ƴan ta’ada zai bada damar zagewa a yi yaki da yan fashin dajin da suke ci gaba da tsananta hare-hare a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Masanan na da ra’ayin cewa ayyana ƴan bindigar a matsayin ƴan ta’adda, zai sa gwamnatin Najeriya ta samu tallafi daga ƙasashen duniya, da kuma ware su daga cikin jama’a don yaki da su ka’in da na’in.

Daga Ahmad Aminu Kado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *