Ni fa har yanzu Ganduje bai biya ni tarar naira 800,000 da kotu ta ce ya biya ba |– Inji Jaafar

A wata tattunawa da shugaban Jaridar Daily Nigerian Jaafar Jaafar yayi da BBC Hausa ya bayyana cewa har yanzu gwamnan Kano Abdullahi Ganduje bai tuntube shi ba game da tarar da Kotu ta umarce shi ya biya shi ba.

Idan ba a manta ba Kotu ta umarci gwamna Abdullahi Ganduje ya biya Jaafar naira 800,000 saboda bata masa lokaci da yayi a Kotu a lokacin da ya janye karar da ya shigar cewa Jaafar yayi masa Kazafi ne sakin bidiyon da yayi da aka nuno shi yana karkacewa yana zura bandir din daloli a aljifan sa.

Sai

dai kuma Jaafar ya bayyana cewa har yanzu gwamna Ganduje bai biya shi kudin ba, sannan Lauyan gandujen ma ya gudu, ba sake ji daga bakin sa ba.

“Daga gwamnan har lauyansa babu wanda na ji duriyarsa har yanzu.”

Mai shari’a Suleiman Danmallam wanda shine ya yanke wannan hukunci, ya umarci gwamnan ya biya Jaafar naira 400,000 sannan ya biya Jaridar sa naira 400,000.

Jaafar na zaune a kasar Birtaniya tare da iyalan sa.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *