RANAR ‘YAN CI: Bayan samun ‘Yan ci Tabbas Mun samu Babban Cigaba a Nageriya ~Cewar Sanata Uba Sani.

A Lokacin da yake aikewa da Sakon taya murna ga ‘yan Nageriya bisa ga Murnar zuwan Ranar Samun ‘yancin Nageriya Sanata Uba Sani Mai wakiltar kaduna ta tsakiya a majalisar dattijan Nageriya ya ce Ina taya ‘yan uwa da abokan arziki a duk fadin duniya, godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya raya kasarmu acikin shekaru 61 da suka gabata. Tabbas Mun samu Babban ci gaba kuma Mun rasa da marmaki da masu tarin yawa. Mun fuskanci manyan kalubale. Amma mun jure. Domin mun kasance mutane ne masu Matukar juriya.

Babban

ƙalubalenmu shine wato ci gaba da tunanin ƙirƙiro wata sahuwar ƙasar Najeriya. Haryanzu Mun kasa sarrafa bambance -bambancen da ke tsakaninmu yadda ya kamata
‘yan tawaye,’ yan fashi, da masu ballewa da masu garkuwa da mutane. Sun lalata al’ummominmu da dama Sun yi asarar rayuka. Sun lalata hanyoyi kala-kala na zamantakewar rayuwar mutane tabbas sun Kasance ba su da hankali Kuma Mugaye ne amma tabbas karshen su yazo.

Wannan ranar tunawa da samun ‘yancin kai wata muhimmiyar rana ce a daidai wannan Lokaci da Muke yaki wasu abubuwa waɗanda suka ƙuduri aniyar juyar da ci gaban da muka samu a matsayin ƙasa da al’umma Amma idan mun Basu dama, domin zamu iya dawo da kwanciyar Hankali da Martabar mu’amullar Yau da kullum Cikin kasarmu ta gado Mai cike da soyayya Gwamnatocin mu da jami’an tsaro sun mayar da Hankali kan masu aikata laifuka Wanda Yanzu suke tserewa Zuwa wani tudun mun tsira tabbas za a dawo da kwanciyar hankali da zaman lafiyar kasarmu Inji Sanatan.

Sanatan Ya kuma Kara da Cewa Ina kira ga ‘yan Najeriya da su ba hukumomin tsaro cikakken goyon baya a ayyukan da suke gudanarwa a duk fadin kasar nan domin taimakon su shine mabuɗin nasara ga Aikin da suke Yi Dole ne mu kasance masu tunatar da juna kuma mu ba da gudummawar ta Hanyar yawanmu domin tabbatar da tsaron al’ummominmu. Dole ne mu fara tattaunawar tsakanin al’umma don gina zaman lafiya mai dorewa a cikin al’ummomin mu domin Babu wani cigaba da zai yiwu a Lokacin da zaman lafiya ya yi karanci.

Ina yabawa gwamna Malam Nasir El-Rufai kan matakan da yake dauka na kan masu aikata muggan laifuka a jihar Kaduna zamu goyi bayansa kwarai da gaske domin tsayar da Cikakkiyar doka mai ƙarfin a Jihar don kawo karshen ta’addancin masu laifi Wanda keyi Cikin nuna alfahari. Tabbas mutanen mu za su samu iskar Yan ci Zaman lafiya Mai kyau.

Daga Karshe Ina jinjinawa mutane na masu daraja na shiyyar da nake wakiltar a Kaduna ta tsakiya musamman a wannan Rana Mai albarka, Kuma Zan ci Gaba da himmatuwa a gare ku domin jindadin ku da ci Gabanku Inji Sanata Uba Sani

Barkanku da Ranar Murnar cika shekara 61 da samun ‘yancin kai.

Sanata Uba Sani,
Kaduna Central Senatorial District

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *