Rashin motoci da makamai yana rage Karfi da kwarjin Sojojin mu a wajen ‘yan ta’adda ~Cewar Janar Farouk Yahaya

Shugaban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Farouk Yahaya, ya ce rashin motocin da ake bukata da kuma makaman da ake bukata domin gudanar da ayyukan ya shafi kwarjinin darajar sojojin.

Ya bayyana hakan ne a taron shekara-shekara na babban hafsan sojin kasa a Abuja ranar Litinin.

Ya ce, “Rashin motocin da ake bukata da dandamalin makami don ba da tallafin da ake bukata domin gudanar da ayyuka ya haifar da mummunan tasiri ga kwazon sojojin Nageriya Kan ta’addanci.

“Don haka, na umurci sashin Depot Engineering Depot da injiniyoyin Sojojin Najeriya na musamman tare da Hukumar NAEME da sauran masu ruwa da tsaki da su duba ciki su ga yadda za a iya tunkarar wadannan kalubale.

Sai

dai ya ce matsalar tsaro a yankin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya wanda har ya zuwa yanzu ba a ta’azzara ba saboda karuwar ayyukan ‘yan bindiga da sauran su a yanzu an samu kwanciyar hankali.
Advertisements

One thought on “Rashin motoci da makamai yana rage Karfi da kwarjin Sojojin mu a wajen ‘yan ta’adda ~Cewar Janar Farouk Yahaya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *