Rundunar Soji Ta Tabbatar da Kamun Wasu Yan Kungiyar Boko Haram a Kano

A ranar Lahadi, 9 a watan Mayu ne rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da samamen da ta kai ga kame wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne a jihar Kano.

Mai magana da yawun runduna ta 3 ta sojojin Najeriya da ke Kano, Kyaftin Njoko Irabor ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai amma bai bayar da takamaiman adadin wadanda aka kama ba.

Kodayake, majiyoyi a yankin sun sanya adadin wadanda ake zargin zuwa 10, jaridar Vanguard ta ruwaito.

An tattaro cewa an kama wadanda ake zargin ‘yan ta’addan ne lokacin da sojojin suka kai mamaya Filin Lazio da ke Unguwar Hotoro a cikin garin Kano a ranar Asabar da yamma don mamaye masallaci da wasu gidaje da ake zargin na wasu ‘yan jihar Borno ne da suka tsere daga yankin arewa maso gabas da ke fama da rikicin Boko Haram.

Kyaftin Irabor ya ce, “Ee, an gudanar da aikin a yankin kuma zai kasance shiri da za a ci gaba da aiwatarwa”.

A daidai lokacin, Kakakin rundunar ya yi alkawarin ba da cikakken bayani kan aikin da kuma yawan wadanda aka kama yayin aikin wanda ya dauki sama da awa guda.

Rahotanni sun bayyana cewa sojojin sun kama mutanen lokacin da suka kutsa Filin Lazio dake yankin Hotoro a cikin garin Kano da yammacin ranar Asabar.

Waɗanda aka kama ɗin sun yi koƙarin kai hari ne a wani masallaci da kuma wasu gidaje dake yankin, sai dai rahotanni sun nuna cewa farmakin yazo dai-dai lokacin da musulmai ke shan ruwa bayan sun kai azumi.

Daga Ahmad Aminu Kado

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *