Sakin baki sakaka a Facebook, akan Ganduje ya tura wani matashi gidan yari.

Wani mutum ya rabauta da tafiya gidan gyaran hali a wata kotun majistire mai lamba 10 da mai Shari’a Muhammad Jibrin yake jagoranta.

Shidai Sadi Bala Lamido, ana tuhumar sa ne, abisa laifin sakin baki babu ƙwaɓa, akan mai girma gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Sadi Bala Lamido, ana zargin sa da yawa dandalin Facebook ne, tare da yin maganganu maras kan gado, da wasu suke zargin cewa, ba da kowa yake ba sai da gwamnan na jihar Kano.

class="wp-block-image size-full">

To koda aka karantawa Sadi Bala Lamido tuhumar da ake masa, ya musanta, yayin da kuma launyan dake kare shi, ya nemi kotu data bada belin sa.

Kotun ta sanya ranar 15 ga watan nan domin lauyan wanda ake karewa yayi suka akan rokon neman belin.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *