Sama da malaman coci-coci dubu ne suke goyon bayan takarar Gwamna Yahaya Bello na kogi a Zaben 2024.

Sama da limaman coci dubu daya ne wanda suka hada da bishops 100 ne ke marawa Gwamna Yahaya Bello na Kogi baya domin tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023, suna masu bayyana shi a matsayin “ zabin Allah.

Malaman addinin za su kuma shirya azumi da addu’o’i na kwanaki uku domin samun nasarar Mista Bello a shekarar 2023, in ji Jonathan Praise, mai kaddamar da ibada a Abuja, a ranar Laraba.

“Manufar taron ita ce samar da garkuwa da goyon baya ga Gwamna Bello, wanda shine zabin da Allah ya zaba domin ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari,” in ji Mista Praise. “Don haka, sama da Bishops 100 da limaman Kirista za su gudanar da addu’o’i da azumi na kwanaki uku don nasarar Bello a 2023.”

Shirin

wanda aka shirya gudanarwa a dandalin Unity Fountain da ke Abuja, zai samu halartar malamai da malaman coci sama da 1,000 daga kowace jiha ta tarayya.

Da yake tunawa da yadda Mista Bello ya tashi ya zama gwamna, ya ce ba haka kawai abin ya faru ba sai dai kaddarar Allah.

“Zai girgiza masu suka a zabe na gaba,” in ji Mista Praise

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *