Sama da naira biliyan 190 gwamnati ta ware don aikin Ƙidayar jama’ar ƙasa a shekarar 2022.

Kwamitin majalisar dattawa mai kula da yawan jama’a da tantance ‘yan kasa a ranar Laraba ya bayyana cewa sama da Naira Biliyan 190 aka ware domin gudanar da ayyukan kidayar Jama’a.

Kwamitin majalisar dattawa mai kula da yawan al’umma da tantance ‘yan kasa a ranar Laraba ya bayyana cewa sama da Naira biliyan 190 aka ware domin gudanar da kidayar jama’a a shekara mai zuwa.

Shugaban kwamatin, Sanata Sahabi Alhaji Yaú ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan kare kasafin kudin 2022 na hukumomin da ke karkashin kulawar kwamitin sa a gaban kwamitin kasafin kudi.

Ya

ce: “Sama da N190bn aka ware domin gudanar da aikin. Muna jiran shugaban kasa ya bayyana lokacin da ayyukan za su fara.”

Game da cewa 2022 shekara ce kafin zaɓe, Yau ya ce: “Sun yi tunanin lokaci ne mafi kyau. Tabbas sun yi lissafinsu kuma shugaban kasa a shirye yake ya gudanar da kidayar jama’a nan da 2022.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *